Ƙungiyar kwadago a Najeriya ta shiya zanga-zangar lumana don nuna rashin amincewa da ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka yi a ƙasar.

Kumgiyoyin NLC da TUC sun dauki matakin zuwa ofisoshin rarraba wutar lantarki da kula da ita don nuna rashin amincewarsu a kai.
Kungiyoyin sun yi zanga-zangar ne yau a jihohin Najeriya.

A jihar Kano ma mataimakin sakataren kungiyar kwadago Abbas Ibrahim ya ce sun ɗauki matakin haka ne ganin yadda aka ƙara kuɗin wutar a ƙasar.

Ya ce ma’aikata ba za su lamunci matakin da gwamnati ta dauka na kara kudin wutar ba.
Kungiyoyin sun gudanar da zanga-zangar yau a dukkanin jihohin Najeriya kuma su ke nema da a janye ƙarin kuɗin wutar da aka yi.
Gwamnatin tarayya ta yi ƙarin kashi 300 na rukunin A da su ke samun wutar na awanni 24 kamar yadda su ka faɗa.