Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci zaman majalisar zartarwa karo na biyar a shekarar 2024.

Kafin zaman da ya gudana a yau, Tinubu ya rantsar da sabbin kwamishinoni biyu a hukumar ƙidaya ta ƙasa.
Kafin biyun da aka rantsar yau, shugaban ya rantsar da wasu 17 a ranar 14 ga watan Maris ɗin shekarar da mu ke ciki.

Daga bisani kuma shugaban ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta kasa a fadrasa.

Daga cikin waɗanda su ka halarci zaman akwai mataimakin shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima, sakataren gwamnatin tarayya, shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya da shugaban ma’aikata na kasa sa sauran ministoci da dama.
Wannan shi ne karo na farko da shugaban ya jagoranci zaman bayan da ya tafi ƙasar saudiyya halartar taro.
Shugaban ya dawo Najeriya bayan da ƴan ƙasar ke tunanin ya shafe lokuta bayan kammala taron.