Al’ummar Anguwan Rimi da ke Zangon Kataf a Kaduna sun shiga cikin zulumi bayan da wasu ƴan bindiga su ka hallaka wani soja tare da yin garkuwa da yin garkuwa da abokiyar zaman mahaifiyarsa.

Sojan da aka hallaka mai suna Yahaya Ayuba an hallakashi kamar yadda guda cikin yan uwansa Kantiok Solomon ya tabbatar a yau Litinin.

Ya ce, sojan ya koma gida ne daga Legas jiya Lahadi, kuma ƴan bindigan su ka shiga gidansa da misalin ƙarfe 11:00pm.

Ya ƙara da cewa a kokarinsu na tafiya da abokiyar zaman mahaifiyarsa tasa ya yi ƙoƙarin hanawa sai su ka kasheshi.

Wani Angelo Takwai ya ce sun yi ƙoƙarin kiran jami’an tsaro don kai musu ɗauki.

Sai dai jami’an yan sanda a jihar ba su magantu a dangane da lamarin ba.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: