Rundunar yan sanda a babban birnin tarayya Abuja sun sha alwashin ci gaba da murkushe ayyukan bata gari da ke addabar jama’a.

Kwamishinan ƴan sanda a Abuja Benneth Igwe ne ya bayyana haka yau yayin da yake holen masu laifi da jami’an su ka kama.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai ƴan fashi da makami, masu satar mota, da sauran masu aikata laifuka daban-daban.

Haka kuma akwai makamai da aka samu daga wanensu da zunzurutun kudi naira 2,230,000.

Sannan an kwato motoci shida, bindigu kirar gida da harsashi.
Daga cikin wanɗanda aka kama akwai wasu ƴan fashi biyar waɗanda ƴan jihar Nassarawa ne.
Annan Kwamishinan ya ce sun fara bincike kan mutuwar wani Khalid Bichi wand aya tabbatar da cewar za su tabbatar sun yi binciken d aya dace a kai.