Gwamnatin jihar Gombe ta ce ta daina raba tallafin kayan abinci ga mazauna jihar, domin kamata ya yi kowa ya dauki fatanya ya noma abun da zai ci.

Gwamna Inuwa Yahaya ne ya bayyana matakin yayin bude wani kamfanin takin zamanin a jihar, inda ya ce lokaci ya wuce da za a dinga tallafawa mutane da abinci.


Gwamna Inuwa Yahaya ya ce duk wanda ba zai noma abin da zai ci ba, to ya hakura da cin abinci kwata-kwata.
Ya ce lokaci ya yi da kowa ya kamata ya daina jira sai an ba shi abinci, domin noma ne mafitar da ya kamata kowa ya runguma a jihar.
Haka zalika ya bayyana cewa an kulle kofar bayar da tallafin abinci a jiharsa, domin ba zai lamunci mutane na zaune suna jiran a ba su abinci ba.
Ya ce gwamnatinsa za ta taimakawa duk wanda ya shirya komawa gona domin noma abinci, amma ba zai kara bayar da tallafin abincin ba.