Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta na kan nazarin yiwuwar fara amfani da wani sabon tsarin biyan albashi ga ma’aikatan gwamnati.

Gwamnati ta ce idan aka fara amfani da sabon tsarin, ma’aikatan da ke a mataki daya za su iya samun albashi daban-daban.


Gwamnatin ta ce za ta fara amfani da tsarin ‘iya aikinka, iya albashinka’ ne saboda ta fahimci cewa ‘yin aiki tukuru kuma mai inganci’ shi ne babban abin da ke kawo ci gaban tattalin arzikin kasar.
Shugaban hukumar samar da ingantaccen aiki ta kasa, Nasir Raji-Mustapha ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai.
Ya ce suna shirin samar da tsarin biyan albashi gwargadon kokarin ma’akaci wanda zai tabbatar da cewa wadanda suka yi aiki tukuru sun samu ladan kokarinsu.
Haka zalika, wannan tsarin ba zai yi la’akari da matakin aiki ba, ma’aikata a mataki daya na iya samun albashi daban-daban.