Jami’an hisba a jihar Kano sun kama wasu matasa guda 20 da ake zargi da aikata badala a wani gidan shakatawa dake titin ring road wanda hakan ya damu mazauna yankin matuka.

Jami’an da ke aiki da bangaren ‘operation kauda badala’ sun kama matasan ne bayan mazauna unguwar sun shigar da kokensu kan yadda ake bata musu unguwa da mummunan aiki.


Mataimakin kwamandan hukumar, Dr. Mujahidin Aminuddin Abubakar, ya bayyana cewa ba karamin laifi matasan su ka aikata ba.
Dr. Mujahidin Aminuddin Abubakar ya yi karin bayanin cewa iyo da zummar shakatawa da matasan su ka yi bai dace ba, kuma da wani aikin ladan su ka yi da ya fiye musu duniya da gobe kiyama.
Hukumar hisba da ke umarni da kyakkyawa da hani da mummunan aiki a jihar Kano ta yi kakkausan tsawatarwa kan matasan da ke murje idanunsu suna aikata ayyukan da musulunci ya yi hani da su.
Ya bayyana cewa hukumarsu na binciken wasu matasa 20 da ake zargi da aikata badala a titin Ring Road da ke jihar.
Ko a baya hukumar ta kama easu mata da laifin sata.
Dr. Aminuddin ya ce da zarar an kammala binciken za a kai su kotu don hukunta matasan dai-dai da laifuffukan da ake zargin sun aikata.