Wata babbar kotun tarayya ta yankewa wasu ‘yan canji 17 a jihar Kano hukuncin zaman gidan yari na watanni shida.

 

Kotun ta daure ‘yan canjin ne saboda su na gudanar da kasuwanci ba tare da lasisin da ya dace ba, wanda ya saba wa sashe na 57 (5) (b) na dokar bankuna da cibiyoyin kuɗi ta shekarar 2020.

 

An yanke wa kowanne mai laifin hukuncin daurin watanni shida ko kuma biyan tarar naira 50,000.

 

Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da Ayuba Ibrahim, Idris Saidu, Idris Usman, Shuaibu Muhammad, Hamisu Ilyasu, da wasu mutum 12.

 

An yanke masu hukuncin ne bayan da suka amsa laifin tuhuma daya da ake yi masu a lokacin da ake karanta masu kunshin tuhumar.

 

Wannan dai na zuwa ne yayin da gwamnatin tarayya ke kara matsin lamba kan ‘yan canji a fadin Najeriya a wani yunkuri na daidaita farashin Naira a kasuwar.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: