Rundunar tsaron hadin gwiwa ta kubutar da fasinjoji 17 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a yankin karamar hukumar Batsari a jihar Katsina.

 

Wata majiya mai tushe daga rundunar sojoji ta bayyana cewa jami’an tsaron sun samu wannan nasara ne bayan samun kiran gaggawa ranar 11 ga watan Mayu.

 

Ya ce dakarun rundunar soji ta Tara ne su ka kai ɗauki bayan samun bayanai tare da haɗin guiwar ƴan sanda, ƴan sa’kai na jiha, mafarauta na musamman da mafarautan Batsari.

 

Da isar dakarun, suka fara musayar wuta da ƴan bindigar wanda ya tilastawa maharan guduwa zuwa dazuka mafi kusa tare da barin waɗanda suka sace a wurin.

 

Majiyar ta ce bayan ceto fasinjojin, jami’an tsaron sun mika waɗanda aka kuɓutar ga jami’an gwamnatin ƙaramar hukumar Batsari.

 

Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin Gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa ta ce tuni aka ƙara tura jami’an sojoji a yankunan domin kakkaɓe ƴan ta’adda.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: