Shugaban kasa, Bola Tinubu ya haramtawa mambobin majalisar zartarwa ta tarayya (FEC), sayen motocin da suka dogara da man fetur.

 

Shugaban ya kuma umarci dukkanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati da su koma sayen motocin da ke amfani da iskar gas din CNG.

 

Tinubu ya ba da umarnin ne a taron majalisar zartarwa daya gudana jiya Litinin inda ya kuma ba da umarnin fara mayar da motoci da janareta da ke amfani da man fetur ko dizal zuwa gas din CNG.

 

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook.

 

Ngelale ya bayyana cewa umarnin ya yi daidai da kudurin Tinubu na tabbatar da tsaron makamashi, samar da kayan aiki, da rage yawan amfani da fetur.

 

Sanarwar an yi mata take da: ‘Shugaba Tinubu ya bada umarnin sayen motocin da ake amfani da gas din CNG.

 

Umurnin na ranar Litinin na daya daga cikin manyan shawarwarin da majalisar ta cimmawa kafin ta dage zamanta na sa’o’i hudu zuwa yau Talata 14 ga watan Mayu 2024.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: