Gwamnan Jihar Kano Injinya Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da shirin fara bai’wa kananu da matsakaitan ‘yan kasuwa mata tallafin Naira 50,000 ga kowacce duk wata a Jihar.

Gwamnan shine ya tabbatar da hakan a shafinsa na X a yau Laraba.
Injinya Abba ya ce matan da za su gajiyar sun fito ne daga kananan hukumomi 44 na fadin Jihar.

Gwamnan ya kara da cewa a kowanne wata za a dunga zakulo mata 5,200 domin ba su tallafin.

Gwamnan Abba ya ce gwamnatin ta Kano za ta dunga kashe Naira miliyan 260 a kowanne wata domin ba da tallafin har wa’adin mulkinsa ya kare.
A cewar gwamnan hukumar sake daidaita rayuwar al’umma ta CRC ce za ta dunga bayar da tallafin, inda za a dunga dauko mata dari-dari daga kowace karamar hukuma a cikin kananun hukumomi 36 na wajen birnin Kano.
Ya yin da za a tallafawa mata dari biyu-biyu daga kowace karamar hukuma a cikin kananun hukumomi 8 na cikin birnin Kano.