Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da belin tsohon gwamnan babban bankin kasa na CBN Godwin Emefiele akan kudi Naira miliyan 300.

Kotun ta amince ta bayar da belin Emefiele ne bayan gurfanar da shi a gabanta akan tuhume-tuhume shida da suka shafi buga sabbin takardun kudi a Kasar ba bisa ka’ida ba.

Kafin bayar da belin na Emefiele Alkalin kotun Mai shari’a Anenih ta umarci Emefile da ya mika takardun tafiye-tafiyensa ga kotu sannan kada ya fita daga kasar ba tare da izinin kotu ba.

Daga karshe Alkaliyar ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Mayu da muke ciki domin ci gaba da shari’ar.

Alkalin ta bayar da belin Emefiele ne bisa, makamancin belin da wata kotu a birnin ta bai’wa Emefiele tare da sanya masa wasu sharudda a lokacin da aka gurfanar da shi a gabanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: