Wata kotun a Kasar siwizalan ta yankewa tsohon ministan gwamnatin Gambia karkashin gwamnatin tsohon mai mulkin kama karya Yahya Jammeh hukuncin daurin shekaru ashirin a gidan yari bayan kama shi da laifin cin zarafin Dan’adam.

 

Kotun tarayya ta masu laifi ta kama Osman Sonko da laifin cin zarafi, azabtarwa tare da daurin karya.

 

Sonko wanda aka kora a gwamnatin Gambia a matsayin ministan harkokin cikin gida, an same shi da laifin fyade.

 

A cewar kotun, dakin gwaji ya kama Osman Sonko da laifukan azabtarwa, fyade da cin zarafin Dan’adam.

 

Dakin gwaji ya karkare cewa Osman Sonko ya aikata dukkan laifukan ne a matsayin wani hari don cin zarafin fararen hula, a karshe kotun ta bada damar daukaka kara.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: