Kwamishinan ilmi na jihar Ribas, Farfesa Chinedu Mmon ya sauka daga kan mukaminsa na kwamishina daga gwamnatin Siminalayi Fubara.

 

Mmon shine mutum na uku da aka nada a matsayin kwamishina yana ajiye aikin sa bayan tsohon kwamishinan Shari’a Farfesa Zacchaeus Adangor, da tsohon kwamishinan kudi Isaac Kamalu sun ajiye aikin su wasu makonni a baya da suka gabata.

 

Da Adangor da Kamalu sun ajiye aikin su bayan umarnin da Fubara ya bayar na sauke darajar su zuwa ma’aikatar ayyuka na musamman karkashin ofishin sa da kuma ma’aikatar samar da ayyuka da bayar da tallafi.

 

Tsohon kwamishinan ya ajiye aikin sa ne ta cikin wata wasika mai kwanan wata 15 Mayu 2024, wanda ya aikewa gwamnan ta ofishin sakataren gwamnatin jihar inda ya bayyana ma’aikatar sa da zama gurbatacciya.

 

Tsohon kwamishinan yace natsattsen wuri yana bunkasa yin aiki tare da samar da abinda ake so, sai dai abin takaici ma’aikatar sa yanzu ta zama gurbatacciya kuma babu yanayi mai dadi da zai ba shi damar gudanar da aiki don bunkasa harkar ilmi a jihar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: