Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi martani ga gwamnatin Bola Tinubu kan karkatar da kuɗaɗen ƴan fansho.

Gwamnatin ta bayyana kudurin amfani da kudaden yan fansho ne domin ayyuka na musamman wajen raya kasa.

Sai dai lamarin ya samu suka a wurin masana da yan siyasar Najeriya.

Hukuma mai kula da kudaden ƴan fansho ta kasa ta sanar da cewa asusun kuɗaɗen fansho ya kai Naira tiriliyan 19.96.

Ministan kudi na kasa, Wale Edun ne ya bayyana cewa gwamnatin za tayi amfani da kudaden wajen yin ayyukan raya kasa.

A cewar ministan za a yi amfani da kuɗaɗen ne domin samar da wadatattun gidaje a Najeriya.

Sai dai masana harkokin kudi sun nuna cewa tsarin dokar kasa bai ba gwamnatin damar amfani da kuɗin ma’aikata ba.

Wani masanin harkokin kudi, Musa Ibrahim ya bayyana cewa cikin abubuwan da doka ta ba gwamnati damar yi da kuɗaɗen yan fansho babu ayyukan da ya ke kokarin yi yanzu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: