Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da kafa sabuwar doka da ta shafi harkokin bukukuwa.

Rahotanni sun nuna cewa dokar ta shafi hana maza masu lura da saka sauti a wuraren taro da aka fi sani da DJ aiki a bukukuwan mata.
Babban kwamandan Hisba na jihar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayar da sanarwar.

Malam Daurawa ya ce manufar dokar ita ce tsaftace jihar kan cakuduwa tsakanin maza da mata ba bisa ka’ida ba.

A matsayin jihar da ake aiki da Shari’a, Daurawa ya ce bai dace a bar maza da mata na cakuduwa da sunan biki ba.
Saboda ana ganin hakan hanya ce da za ta kawo yaɗuwar fasikanci a cikin al’ummar jihar Kano.
Sai kuma ya kara da cewa daga yanzu mata masu aikin DJ ne za su rika gudanar da hidimar bukukuwan mata ƴan uwansu.