Hukumomi a jihar Lagos sun dauki gagarumin aikin tsaftace gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba a yankin Lekki.

Kwamitin kar-ta-kwana da Gwamnatin jihar ta kafa domin gudanar da aikin karkashin jagorancin CSP Shola Jejeloye zai rushe dakunan da aka gina a yankin.

CSP Shola Jejeloye ya bayyana cewa idan an rushe daruruwan gine-ginen, ana sa ran zai taimaka wajen kakkabe ayyukan bata-gari a yankin.

Shugaban kwamitin kar-ta-kwana, CSP Shola Jejeloye ya bayyana cewa sun kama wasu masu babura da ke bin titunan Victoria Island, da Bourdillon.

Haka zalika baburan suna bin hanyoyin Falomo, da Ikeja, da Abeokuta Expressway, da Ojodu Berger, da Fagba, duk da hana su da gwamnati ta yi.

Ya ce an kama baburan haya guda 220, kuma za su ci gaba da tilasta cewa matuka baburan har sai an bi dokar gwamnati.

CSP Shola Jejeloye ya gargadi matuka baburan da su guji karya dokar gwamnati domin tsaftace hanyoyin da ke jihar Lagos.

Leave a Reply

%d bloggers like this: