Jirgin alhazan farko daga jihar Kebbi ya tashi zuwa ƙasa mai tsarki kamar yadda aka tsara domin sauke faralin aikin hajji a wannan shekara ta 2024.

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ne ya tabbatar da haka a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Laraba.
A sanarwar da gwamnan ya wallafa, ya ce an kaddamar da fara jigilar alhazan Najeriya zuwa ƙasar Saudiyya a filin jirgin saman Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi.

Gwamnan ya kuma gode wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima bisa gagarumin goyon bayan da suka bayar a aikin Hajjin 2024.

A cewarsa goyon bayan da suke bayarwa don samun nasarar wannan aikin ibada ya ƙara nuna muhimmancin aikin a addinin Musulunci.
Nasiru Idiris ya kuma yabawa hukumar NAHCON bisa zaɓen jihar Kebbi a matsayim wurin da ta kaddamar da fara jigilar mahajjata zuwa ƙasa mai tsarki.
Ya kuma roƙi alhazan kar su manta su sanya Najeriya da shugabannin ƙasar nan a addu’o’in su.