Rundunar sojin Najeriya sun gano rijiyoyin mai biyar da barayin danyen mai suka haka a jihar Ribas.

Sojojin sun sanar da kama masu satar danyen man ne da litar mai 45,000 a jiya Laraba, 15 ga watan Mayu.

Da yake jawabi a madadin kwamandan rundunar, Laftanal Kanal Ishaya Manga ya ce barayin danyen man suna amfani da tukwane wurin tace shi.

Laftanal Kanal Ishaya Manga ya kara da cewa nasarar da suka samu ta samo asali ne daga farautar barayin da suka fara tun watan Fabrairu.

Ya tabbatar wa yan jarida cewa akwai wasu ramukan da bata garin suke cigaba da boye danyen mai a ciki amma sannu a hankali rundunar za ta cimma musu.

Laftanal Kanal Ishaya Manga ya yi godiya ga mutanen yankin kan cigaba da goyon baya da suke basu wurin yaki da barayin.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: