Kungiyar kwadago a Najeriya sun yi fatali da tayin Gwamnatin Tarayya kan mafi karancin albashi.

Kungiyoyin sun ce kwata-kwata babu manufa kan gabatar da naira 48,000 da gwamnatin ta yi a matsayin mafi karancin albashi.

Shugaban kungiyar TUC a Najeriya Festus Osifo ya bayyana haka a jiya Laraba 15 ga watan Mayu yayin hira da Channels TV.

Kwamred Osifo ya caccaki gwamnatin inda ya ce kwata-kwata ba ta shirya tattaunawa da ma’aikata ba.

Ya ce kananan ma’aikatan Gwamnatin Tarayya na karbar N77,000 a wata sannan a gabatar da N48,000 abin takaici ne.

Ya ce kafin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bar mulki, karamin ma’aikaci a Gwamnatin Tarayya yana karbar N42,000 a wata.

Osifo ya kalubalanci gwamnatin ta kawo wani tsari da N48,000 zai isa ma’aikaci a wata ba tare da wata matsala ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: