Rundunar ‘yan sanda a Jihar Kwara ta kama wasu jami’an lafiya biyar kan batar da mahaifa da cibiya bayan karbar haihuwar a wani asibiti a Jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Ejire Adeyemi ce ta tabbatar da faruwar lamarin a yau Juma’a.

Kakakin ta ce lamarin ya faru ne a asibitin Iloffa da ke cikin karamar hukumar Oke-Ero a jihar a karshen makon da ya gabata.

Kakakin ta kara da cewa sun kama jami’an lafiyar ne bayan wanda ta haihu ta bukaci jami”an su gabatar mata da mahaifa da kuma cibiya bayan haihuwar jaririnnata, inda suka gaza gabatar mata wanda hakan ya sanya tashigar da kara ga jami’ansu.

Sai dai kakakin ya ce bayan tuhumar wadanda ake zargi sun bayyana cewa sun jefar da mahaifar amma suna tsammanin kare ya cinye ta.

Matar da ta shigar da karar ta bukaci da rundunar ‘yan sandan ta zurfafa bincike akan lamarin tare da yiwa jami’an hukunci akan abinda suka aikata.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: