Hadakar jami’an tsaron yan sanda da na DSS a Jihar Delta sun kama wasu mutane uku ciki harda wani dan kasar Kamaru da ake zargi da yiin garkuwa da mutane a Najeriya.

Kakakin yan sandan jihar Edafe Bright ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Rundunar ta bayyana cewa ana zargin mutumin dan kasar ta Kamaru ya hadaka kai ne da wasu ‘yan Najeriya su biyu wajen aikata ta’addanci a Jihar ta Delta.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa sauuran muutanen da suka hada kai da dan kasar ta kamaru daya dan asalin Jihar Kaduna ne, yayin da dayan ya kasance dan asalin Jihar Kogi.

Rundunar ta bayyana cewa ana zargin mutanen ne da aikata laifin yin garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci a wasu yankuna na Jihar.

Rundunar ta bayyana cewa bayan kama mutanen jami’an sun yi nasarar kwato makaman da mutanen ke aiki da su ciki har da bindiga guda biyu da kuma wuka.

Rundunar ta ce ya zuwa yanzu su na ci gaba da gudanar da bincike domin kama sauran masu aikata ta’adda a Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: