Wata hatsaniya ta barke tsakanin jami’an hukumar DSS da ma’aikatan majalisar tarayya a birnin tarayya Abuja.

Lamarin ya faru ne da jami’an na DSS da wasu manyan ma’aikatan majalisar biyu a kofar shiga sashin White House da ke zauren majalisar tarayya.
Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya barke ne da misalin karfe 11:45 na safiyar yau Jumu’a a kofar da ta raba sabon ginin majalisar dattawa da sashin White House.

Rahotan ya kara da cewa lamarin ya faruu ne a lokacin da jami’an na DSS da ke tsaron kofar sashin suka nemi ma’aikatan na NASS da su bayar da katinsu na shaidar shiga gurin kafin su wuce.

Sai dai wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa kafin yunkurin jami’an na shiga cikin White House sai da suka nunawa jami’an katinnasu.
Ganau din ya kara da cewa duk da nunawa jami’an katin da su ka yi suka hanasu shiga kan cewa ba su gabatar da kansu yadda ya kama ba.
Inda ya ce hakan ne ya haifar da rikicin a tsakanin bangarorin biyu bayan tafiya da su ofishinsu da su yi.