Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar bayar da belin jami’in kamfanin Binance Tigran Gambaryan.

Kotun ta ki bayar da belin jami’in kamfanin ne a wani zama da kotun ta gudanar a yau Juma’a wanda Mai shari’a Emeka Nwite ya jagoranta.
A yayin yanke hukuncin Alkalin ya bayyana cewa kotun ta ki bayar da belin Gambaryan ne bisa kyautata zaton zai iya tsallake sharuddan beli da aka sanya masa bayan an sake shi kamar yadda shugaban kamfanin na Banance ya yi a lokacin da ake tsare dashi.

An gurfanar da jami’in kamfanin na Binance ne bisa zarginsa da ake yi da safarar kudaden haram a Najeriya.

Daga karshe alkalin ya bayar da umarnin gabatarwa da kotun dukkan abinda ya dace dangane da shari’ar da ake yiwa jami’in na Banance bayan hukumar yaki da masu yiwa tattain arzikin kasa zagon kasa na EFCC ta gurfanar da shi a gabanta.