Kungiyar masu sayar da shanu a kasuwar Kara da ke Bukuru a Jihar Filato sun koka akan yunkurin da ake yi na canza musu guri da gwamnatin Jihar za ta yi.

Kungiyar ta koka ne bayan wa’adin makonni biyu da gwamnatin Jihar ta ba su kan su tashi daga cikin kasuwar.

Kungiyar masu sayar da shanun ta bayyana cewa yankin Gero da Sabongida da gwamnatin ta ce shirin mayar da su yanki ne da ake fama da rikicin kabilanci, wanda hakan barazana ce ga masu saye da sayarwa a yankunan.

Kungiyar ta kuma yi kira da gwamnatin Jihar ta sake yin duba akan lamarin masu sayar da shanu akan yunkurin da ta ke yi na sauya musu gurin zama.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a ranar Litinin din da ta gabata ne gwamantin Jihar Filato ta ba su wa’adin tashi daga cikin kasuwar ta kara.

Umarnin na gwamnatin Jihar na zuwa ne ta hannuun hukumar kula da cigaban garin Jos.

Hukumar ta ce an tashi masu sayar da shanu a kasuwar ne domin gwamnatin Jihar ta gina filin wasa a gurin da su.

 

Break

 

Wata hatsaniya ta barke tsakanin jami’an hukumar DSS da ma’aikatan majalisar tarayya a birnin tarayya Abuja.

Lamarin ya faru ne da jami’an na DSS da wasu manyan ma’aikatan majalisar biyu a kofar shiga sashin White House da ke zauren majalisar tarayya.

Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya barke ne da misalin karfe 11:45 na safiyar yau Jumu’a a kofar da ta raba sabon ginin majalisar dattawa da sashin White House.

Rahotan ya kara da cewa lamarin ya faruu ne a lokacin da jami’an na DSS da ke tsaron kofar sashin suka nemi ma’aikatan na NASS da su bayar da katinsu na shaidar shiga gurin kafin su wuce.

Sai dai wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa kafin yunkurin jami’an na shiga cikin White House sai da suka nunawa jami’an katinnasu.

Ganau din ya kara da cewa duk da nunawa jami’an katin da su ka yi suka hanasu shiga kan cewa ba su gabatar da kansu yadda ya kama ba.

Inda ya ce hakan ne ya haifar da rikicin a tsakanin bangarorin biyu bayan tafiya da su ofishinsu da su yi.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: