Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Ganduje ya ce tsare-tsaren Shugaban Kasa Bola Tinubu za su inganta Najeriya nan bada dadewa.

Ganduje ya bayyana hakan ne a yau Juma’a a Abuja a yayin karbar bakuncin kungiyar shugabannin kananan hukumomi.
Ganduje ya ce Tinubu zai inganta Najeriya ne bisa yadda yake da jajircewa a siyasa da sauran fanni daban-daban.

A yayin jawabinsa Ganduje ya bayyana cewa a halin yanzu jam’iyyar APC ta fi kowace jamiyya samun yawan Jihohi da kananan hukumomi a Kasar sakamakon kyawawan tsare-tsaren da ta ke dashi.

Shugaban jamiyar ya kuma jinjina tare da yabawa shugabannin kananan hukumomin inda ya bayyana su a matsayin kashin bayan jam’iyyar ta APC bisa kusancinsu da alummar kasa.
Sannan Ganduje ya mika gdiyarsa da shugabannin kananan hukumomin bisa gudunmawar da suke bai’wa jamiyyar.