Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya shugaba Tinubu murnar cikarsa shekara guda akan mulki Kasar.

Buhari ya taya murnar ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata.

Tsohon shugaban ya bukaci ‘yan Najeriya da su sanyawa gwamnatin Tinubu albarka domin ganin ta samu nasarar tafiyar da mulkinta yadda ya kamata.

Kazalika Buhari ya kuma sake bukatar ‘yan kasar da su goyawa gwamnatin ta Tinubu baya domin ganin ta samu nasara.

Daga karshe Buhari ya yiwa gwamnatin ta Tinubu fatan alkhari tare da fatan kammala wa’adin mulkinsa cikin nasara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: