Hukuma mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta tabbatar da kama wani matashi a Jihar Gombe da ake zargi da cin zarafin kudin Najeriya.

Hukukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X a yau Laraba.

Hukumar ta ce ta kama matasgin ne a lokacin da ta samu wani faifan bidiyon matashin yana rawa yana lika naira 200 a wani gidan rawa da ke Tufure a Jihar.

EFCC ta ce bayan samun bidiyon ta gudanar da binciken harta kai ga ta kama matashin.

Sai dai Bayan da hukumar ta kama matashin mai suna Zakariyya Muhammad ya amsa laifin da ake zarginsa.

Hukumar ta bayyana cewa bayan zurfafa bincike akan matashin za ta gabatar da shi a gaban kotu domin yi masa hukunci.

Idan baku manta ba dai koda a baya sai da hukumar ta taba kama wani mutum akan zarginsa da cin zarafin kudiin Najeriya.

Inda hukumar ta ce ba za ta saurarawa dukkan wanda ta kama yana cin zarafin kuudin Kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: