Gwamnatin tarayya ta bayyana dawo da shirin bayar da tallafin kudi ga ‘yan Kasar domin rage musu radadin halin da suke ciki.

Ministan kudi na Kasa Wale Edun ne ya bayyana hakan a Abuja a wajen wani taron ministoci kan cikar shugaba Bola Tinubu shekara guda akan karagar mulkin Kasar a ranar Talata.
Edun ya ce shirin zai ringa tallafawa ‘yan Kasar miliyan 75 kai tsaye, har cikin gidaje miliyan 50 na Kasar domin rage musu radadin halin kuncin da suke ciki.

Ministan ya bayyana cewa kafin dawo da shirin sai da aka yi masa gyaran fuska wanda ake sa ran hakan zai magance zamba cikin aminci.

Edun ya ce gwamnatin ta tarayya ta dawo da shirin ne domin agazawa marasa karfi domin fitar da su daga cikin halin da suke ciki.
Idan ba a manta ba dai gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin ne bayan da ta gano rashin gaskiyar da ake tafkawa a wajen gudanar da shirin bayar da tallafin.