Kungiyar lauyoyi ta Kasa NBA ta nuna rashin jin dadinta dangane da yadda kotuna biyu a Kano suka yanke hukunci mai kama da juna akan masarautar Kano.

Shugaban kungiyar Yakubu Maikyau ne ya bayyana bayyana rashin jindadin kungiyar kan lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Kungiyar ta nuna takaicinta akan yadda kotun tarayya ta yanke hukunci, sannan babbar kotun Jiha itama ta yanke wani hukunci irin na kotun baya.

Kungiyar ta ce hakan babban abin kunya ne yadda kotunan suka ringa yanke hukunci akan masarautar kano, wanda hukuncin ya kasance cin fuska ne ga bangaren shari’a a Kasar.

Channels TV ta rawaito cewa sanarwar da kungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun sakataren yada labaranta Akorede Lawal ya ce yin hakan babban kuskure ne kuma hakan ya kawo babban nakasu ga bangaren shari’a a Najeriya.
A sanarwar shugaban kungiyar ya ce bangaren shari’a zai dade kafin ya farfado daga illar da aka yi masa ganin yadda alkalai da lauyoyi suka gudanar da sharia’ar masarautar Kano.
Shugaban kungiyar ya umarci alkalan da suka ringa yanke hukunci cikin gaggawa da su gaggauta komawa baya domin ganin yadda suka gudanar da ayyukansuu da nufin kawo gyara domin kubtar da kimar shari’ar Kasar.
Sannan ya ce za su hukunta wadanda suka saba dokar aikin.