Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa jami’an sun hallaka ‘yan bindiga 30 a wasu hare-haren da suka kai musu a jihohin Katsina da Borno.

Daraktan yada labaran rundunar Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Laraba a Abuja.
Rundunar ta ce sojojinta na Operation Hadarin Daji da Operation Hadin Kai ne suka kai hare-haren a sansannin ƴan ta’addan a jihohin Kasar.

Edward ya ce harin da jamiannasu suka kai maboyar ‘yan ta’addan a ranar 27 ga watan Mayu, ya yi sanadiyyar kawo karshrn wasu daga cikin ƴan ta’adda da ke goyan rikakken dan ta’adda Babura.

Kakakin ya bayyana cewa an kai hare-haren ne a kusa da wasu kauyukan Bakai, Bakarya,da kauyen Ƴartsintsiya da ke cikin karamar hukumar Kankara ta Jihar Katsina.
Edward ya ce a yayin harin dan ta’adda Babura da kyar ya tsira, yayin da aka hallaka mafiya yawa daga cikin yaransa.
Ya kara da cewa jami’ansu sun kuma sake kai hare-hare makamancin wannan ta sama duk a ranar a maboyar ‘yan ta’adda da ke Tumbun Fulani da ke kusa da tafkin Chadi a Jihar Borno.