Nigerian soldiers march during 58th anniversary celebrations of Nigerian independence, in Abuja, Nigeria, Monday, Oct. 1, 2018. (AP Photo/Olamikan Gbemiga)

Helkwatar tsaro a Najeriya ta ce ta samu nasarar hallaka ƴan bindiga 640, sannan sun kama 1,051 tare da kuɓutar da mutane 563 cikin wata guda.

 

Da yake yi wa manema labarai ƙarin haske, Daraktan yaɗa labarai Edward Buba yau a helkwatar tsaro da ke Abuja.

 

Ya ce an kama wasu daga cikin ƴan bindiga da masu kai musu makamai da kuma masu basu bayanan sirri.

 

Ya ƙara da cewa an ƙwato makamai 707, da harsashin bindiga guda 16,487, sai bindigu ƙirar AK47 guda 411, da wasu bindigun ƙirar gida.

 

Sannan jami’an Operation Haɗin Kai sun kama wani babban mai ƙera bam a dajin sambisa.

 

Haka kumaa akwai mayaƙan Boko Haram da ISWAP 1,099 da su ka miƙa wuya ga jami’an soji cikin wata guda, daga ciki akwai iyalansu sannan sun miƙa bindigu ƙirar AK47 guda 200 da wasu bindigu ƙirar gida.

Leave a Reply

%d bloggers like this: