Jami’an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa a Najeriya EFCC sun kama wasu mutane biyu bisa zargin bai wa jami’insu cin hancin naira miliyan 1,200,000.

 

An kama Faleti Waheed da Noah Olalekan a jihar Oyo.

 

Hakan na kunshe a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Dele Oyewale mai magana da yawun hukumar shiyyar Illorin.

 

Ya ce an kama mutanen ne a ranar Juma’a a Ogbomoso da ke jihar Oyo.

 

Sannan jami’an sun kama wasu mutane bakwai bisa zargin haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

 

Bayan binciken da su ka yi aun gano cewar wadanda aka kama baa su da lasisin hakar ma’adanai, sannan ba su da wata shaidar sahalewa daga mahukunta.

 

Sannan sun gano kuɗi naira 995,500 daga wajen Waheed yayin da aka gano naira 201,000 daga Olalekan.

 

Hukumar ta ce za ta gurfanar da waɗanda ta kama a gaban kotu bayan kammala bincike.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: