Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sake sanya ranar Juma’a 31/5/2024 domin sake ganawa da ƙungiyoyin kwadago a ƙasar.

 

Gwamnatin ta aike da wasika ga kungiyar TUC da NLC domin gayyatarsu taron da za su sake yi a gobe Juma’a.

 

Takardar na ɗauke da sa hannun Ekpo Nta sakataren kwamitin da ke kula da ƙarin albashin ma’aikatan.

 

Za a sake zaman ne domin tattauna batun mafi karancin albashi wanda ake kai ruwa rana a kai.

 

A zaman da gwamnatin ta yi na ƙarshe ta yi wa ƙungiyoyin tayin naira 60,000 a matsayin mafi karancin albashi, sai dai kumgiyar ta yi watsi da hakan inda ta ke neman a biya sama da naira 494,000.

 

A baya, ƙungiyoyin sun buƙaci a biya naira 615,00 sai dai daga bisani su ka sassauta zuwa naira 494,000.

 

Batun ƙarin mafi ƙarancin albashi dai ya sake tsami ne bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana cire tallafin man fetur tun bayan da aka rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: