Kotun ƙoli a Najeriya ta bai wa jihohi mako guda domin su gabatar da bayanan kariya dangane da ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar da su a gabanta.

Gwamnatin tarayya ta shigar da ƙara gaban kotu kan ƙin amincewar gwamnonin jihohi bai wa ƙananan hukumomi damar cin gashin kansu.


A ƙunshin ƙarar, gwamnatin tarayya na son jihohi su bai wa ƙananan hukumomi damar cin gashin kansu.
Sannan kotun ƙoli ta bai wa alƙalin alƙalai na ƙasa kwanaki biyu ya gabatar da nasa bayanin bayan jihohin sun miƙa takardun kariya.
Kotun mai alƙalai bakwai ƙarƙashin mai shari’a Garba Lawal shi ya yi umarnin bayan da gwamnatin tarayya ta shigar da ƙarar.
Sai dai jihohin Kano, Borno, Kogi, Neja, Ogun, Osun, Oyo da Sokoto ba su halarci zaman ba.
Kotun na son kammala shari’ar cikin makonni biyu.
Gwamnatin na son jihohi su bai wa ƙananan hukumomi damar cin gashin kansu, tare da raba asuaun da gwamnatin ke aikewa da kuɗi.
Batun da wasu gwamnonin Najeriya su ka ƙi na’am da shi.