Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ƙara ƙaimi a harkokin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.

 

Shugaban ya bayyana haka ne yayin ƙaddamar da helkwatar ƙwararrun jami’an tsaron ƙasar a Abuja.

 

Tinubu wanda ya samu wakilcin shugaban majalisar dattawan ƙasar Godswill Akpabio, ya ce babban burinsa bai wuce ganin ya karfafi jami’an tsaron soji, hukumar leƙen asiri da jami’an tsaron farin kaya da kuma ƙwararun jami’an tsaron kasar.

 

Ya ce ba ahi da wani tunani da ya wuce ceto ƙasar daga halin da ta shiga.

 

Ya ƙara da cewar koƙarinsa a kullum bai wuce daƙile matsalar tsaro a shiyyoyi ahida na ƙasar da ma ƙasa baki ɗaya.

 

Sai dai ya ce ƙasar na fuskantar ƙalubalen tattalin arziƙi da na fasahar zamani.

 

Tinubu ya sha alwashin inganta walwalar jami’an tsaro da kuma basu horo da kayan aiki har ma da sauran kayayyaki da su ke buƙata.

 

Sannan ya yabawa shugabancin hukumar na baya da na yanzu, bisa ƙoƙarin da su yi har zuwa wannan lokaci.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: