Babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta dage sauraron karar da tsohon gwamnan Jihar Nasir El’Rufa i ya shigar da majalisar dokokin Jihar da Antoni Janar na Jihar a gabanta.

El’Rufa i ya shigar da karar ne bisa kalubalantar rahotan kwamitin Majalisar wanda ya zarge shi da cin hanci da rashawa da kuma yin sama da fadi da dukiyar mutanen Jihar.


Kotun ta fara sauraron karar ne a yau Litinin, inda Lauyan Majalisar Sani Kalu SAN ya bayyanawa kotun cewa su na shirye-shiryen gabatar da takardar farko ta kin amincewa da kotun ba ta da hurumin sauraron karar da El’Rufa i ya shigar gabata.
Kalu ya kuma bukaci kotun ta kara musu lokaci su kammala tattara takardun bukatarsu akan karar tsohon gwamnan na Kaduna.
Bayan rokok lauyan shima lauyan kwamishina kuma Antoni Janar na Jihar Sule Shu’aibu SAN ya goyi bayan bukatar Kalu.
Lauyan Mai kara Sule Umoru bai yi fatali da rokon karin lokacin ba.
Bayak kammala sauraron dukkan hujjojin lauyoyin, Alkalin kotun mai shari a Rilwan M Aikawa ya dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga watan Yulin da muke ciki domin ci gaba da sauraron karar.
Idan baku manta ba tun a ranar 26 ga watan Yuni da ya gabata El’Rufa i gaban kotun inda yake nema kotun ta soke rahotan kwamitin sakamakon tauye masa hakkokinsa da kundin tsarin mulki ya tanada.