Wasu ‘yan ta’adda sanye da hijabi a Jihar Katsina sun yi garkuwa da mutane 26 a karamar hukumar Safana da ke Jihar.

Maharan sun yi garkuwa da mutanen ne a karshen makon da muka yi bankwana da shi a kauyen Runka da ke cikin karamar hukumar ta Safana a Jihar.

A yayin garkuwa da mutane mafiya yawa daga cikin su mata ne da kananan yara.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun je yankin ne da misalin karfe 10:30 na dare, inda kuma zuwan su ke da wuya suka fara harbe-harbe.

Mazaunin garin ya kara da cewa a gidanshi maharan sun yi garkuwa da mata Goma da maza biy, da kuma wasu mutane 14 na daban.

A cewar mazaunin garin hare-haren na faruwa ne sanadiyyar masu kai’wa ‘yan bindigar bayanan sirri wanda hakan ke kara dakula kokarin gwamnati na kawo karshen ‘yan ta’addan.

A yayin tabbatar da faruwar lamarin shugaban karamar hukumar ta Safana Abdullahi Sani, ya tabbatarwa da manema labarai faruwar lamarin, ya ce maharan sun yi garkuwa da mutane 22 amma wasu sun kubuta.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Abubakar Sadik Aliyu bai ce komai ba game da faruwar lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: