Kamfanin mai a Najeriya NNPC ya magantu dangane da dogon layi da ake fama a wasu gidajen man sanadin karancinsa a Najeriya.

Shugaban sashen sadarwar a kamfanin Olufemi Soneye ne ya sanar da haka wanda ya ce hakan na da nasaba da yanayin damina da ake samun yawan walkiya ne ya haifar da ƙarancin man.

A cewarsa, lamarin ya shafi manyan jiragen da ke jigilar man fetur din zuwa ƙananan jiragen ruwa.

Haka kuma akwai ambaliyar ruwan sama da aka samu wanda wannan bangaren ya shafi manyan motocin dakon mai.

Sai dai kamfanin na kokari wajen ganin kawo karshen karanci da wahalar man da ake fuskanta a kwanakin nan.

A yan kwanakin nan dai ana fuskantar layi a wasu gidajen mai a Abuja, Kano Kaduna da wasu jihohi sanadin karancin man fetur da mutane ke amfani da shi yau da kullum.

Leave a Reply

%d bloggers like this: