Wasu rahotanni sun bayyana cewa wasu da ba a san ko suwaye ba sun cinna wa fadar Sarkin Kano Sarki Muhammadu Sanusi II wuta.

Wata majiya daga fadar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a dare ranar Juma’a da misalin karfe 11 na dare.
Majiyar ta bayyana cewa wutar ta haifar da konewar gurin da sarki ke zama domin gudanar da zaman fada a dukkan ranar Litini.

Majiyar ta kara da cewa kofar Kudu da aka sanywa wutar tana da kofa ciki da waje, inda aka balle makullin ƙofar tare sanya wuta daga bisa kuma suka rufe.

Acewarta wutar ta kone karagar sarkin da na’urar sanyaya daki wata Asi da kuma sauran kayayyakin da ke cikin dakin.
Sai dai da aka nemi jinta bakin mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara na Kano, Saminu Yusif Abdullahi dangane da faruwar lamarin, ya bayyana cewa ba su da rahotan kan lamarin sakamakon ba su samu kiran waya dangane da lamarin.
Anashi bangaren Shugaban Ma’aikatan Fadar Sarkin Munir Sanusi Bayero Dan Buram Kano ya tabbatar da faruwar lamarin ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
A sanarwar da Munir din ya fitar, ya ce da safiyar yau Asabar 13 ga watan Yuli 2024 wutar ta tashi a kotun Sarki da ke kofar Kudu a Jihar.
Munir Sanusi ya ce babu wanda ya jikkata kuma barnar da wutar ta yi babu yawa.ya ce ya zuwa yanzu ana ci gaba da gudanar da binciken domin gano dalilin tashin gobarar tare da daukar mataki akai.