Majalisar wakilai a Najeriya ta buƙaci shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta cire shugaban hukumar kula da mai ta ƙasa.

 

Hakan na zuwa ne bayan da majalisar ke fara bincike dangane da zargin da ya ke yi wa matatar mai ta Dangote na cewar gas din daa yake fitarwa ba shi da inganci.

 

Kudirin dai ya fito ne daga bakin dannmajakisa daga jihar Edo Esosa Iyawe.

 

A zaman majalisar na yau, majalisar ta fara duba tare da bincike a kan dambarwar da ke tsakanin hukumar kula da mai ta ƙasa da fitaccen attajirin nan Alhaji Aliko Dangote.

 

A jiya Litinin ne karamin ministan man fetur ya yi wata ganawa da bangarorin da wasu masu ruwa da tsaki don daidaita lamarin.

 

Dangote ta zargi wasu ma’aikatan NNPC da wasu a ƙasar da ma kasashen ketare da hannu wajen hana ruwa gudu a tafiyar da matatar man sa.

 

Hakan na zuwa ne bayan da ya ce zai fara fitar da man fetur a watan Agusta mai kamawa.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: