Rundunar yan sandan Najeriya ta ce za ta magantu a kan zanga-zangar da ake shiryawa a ƙasar.

 

Babban sufeton yan sanda na ƙasa Kayode Egbetokun ne ya bayyana haka yau a Abuja.

 

Ya ce za su yi bayani a kan zanga-zangar cikin kwarewa da kayakkawan lafazi.

 

A yayin wata ganawa da manyan jami’an yan sanda, ya gana da manyan yan sanda daga sassan kasar daban-daban.

 

Ganawar ta mayar da hankali ne domin duba hanyar da za a bi don shawo kan batun zanga-zangar da ake shiryawa.

 

Sufeton yan sandan ya ce idan har zanga-zangar lumanaa ce za su yi aikin kare masu zanga-zangar domin ya na daga cikin ayyukansu na tsare rayuwa lafiya da dukiyoyi.

 

Ya ce ba sa adawa da yin zanga-zanga kuma za su bayar da kariya ga masu yinta matuƙar ta lumana ce.

 

Sai dai inda matsalar ta ke idan har ya zamto ba zanga-zangar lumana ba ce.

 

Wasu matasa ne dai ke ƙoƙarin shirya zanga-zanga a Najeriya bisa tsadar rayuwa da yunwa da matsalar tsaro da ake fama a ƙasar

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: