Hukumar da ke shirya jarrabawa kammala makarantun Sakandire WAEC ta sanar da fitar da sakamakon jarrabawar ta shekarar 2024.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinta na X a yau Litinin.

Sanarwar ta bayyana cewa hukumar shirya jarrabawar Afirka ta Yamma tana farin cikin sanar da daliban suka rubuta jarrabawar ta WASSCE a shekarar 2024 cewa ta fitar da sakamakon jarabawar a yau Litinin.

Sanarwar ta kuma bukaci daliban da suka rubuta jararrabar da su duba sakamakon jarabawar ta su.

Akalla dalibai 1,814,344 ne na makarantun sakandare 22,229 a fadin kasar suka rubuta jarrabawar a shekarar bana.

Hukumar ta ce daliban za su suba sakamakonnasu ne ta hanyar amfani da wayoyin hannu ko kwamfuta, sannan su shiga shafin hukumar na yanar gizo www.waecdirect.org.

Daga bisani ta ce bayan daliban sun shiga za su rubuta lambar jarrabawarsu da watan da suka runuta jarabawar da kuma shekara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: