Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanya dokar ƙarin albashi ga alkalai da ma’aikatan Shari’a a ƙasar.

Hakan na kunshe a wata sanarwa da Bashir Garba Lado mai bashi shawara kan harkokin majalisar dattawa ya fitar.
Sanarwa ta ce saka hannun da shugaban ya yi na daga cikin ƙudirin gwamnatin sa na kyautatawa da kulawa da walwalar ma’aikata.

Dokar dai ta bayar da damar karin kashi 300 a alashin ma’aikatan Shari’a.

Tun a watan Yuni majalisar dokoki ta ƙasa ta amince da karin tare da aikewa da shugaban ƙasa don sanya hannu.
Dokar dai za ta bayar da dama don karin albashi da alawus alawus ga ma’aikatan Shari’a.
Tuni dai mahukunta a Najeriya ke ganin tabarbarewar bangaren shari’a na taka awa wajen yaduwar rashawa a ƙasar.