Wasu jami’an ƴan sanda sun koka a kan yadda aka ƙi biyansu alawus alawus din su.

 

Jami’an sun yi zanga-zanga tare da zuwa cibiyar ƴan jarida a jihar Akwa Ibom.

 

Yan sandan wadanda mafi yawa masu muƙamin isfekta ne, sun koka a kan kin biyansu alawus tsawon watanni 11.

 

Su ka ce sun hura su 1,500 da su ka samu ƙarin girma tun a watan Satumban shekarar 2023 da a gabata.

 

Sai dai har zuwa yanzu ba a ƙara musu albashi ba kuma ba a biyansu alawus alawus din su.

 

Jami’an sun mika koken a babban sufeton yan sanda na ƙasa da majalisar dokoki da fadar shugaban ƙasa.

 

Su ka ce ba sa jin daɗin yadda su ke tafiyar da aikin ba tare da ji dadin walwalarsu ba.

 

Haka kuma babu wata hanya da zasu bi illa nuna damuwarsu ga mahukunta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: