Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bai’wa hukumar da ke karbar korafe-korafen jama’a da yaki da rashawa ta Jihar (PCACC) umarnin gudanar da bincike akan zargin cewa an bayar da kwangilar samar da magunguna a kananan hukumomi 44 na fadin Jihar.

Gwamna Abba ya kuma bayyana cewa bashi da masaniya akan kwangilar da aka ce an bayar a kwanakin baya, wadda aka bai’wa wani mai suna Musa Garba Kwankwaso wanda ake zargi ɗan uwa ne ga tsohon Gwamnan Jihar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yau Lahadi ta cikin wata sanarwar hadin gwiwa da Kwamishinan yada Labarai na Jihar Baba Halilu Dantiye, da kuma Mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa suka fitar.

Jami’an gwamnatin sun fitar da sanarwar ne , bayand da shahararn dan barkwancinan a shafukan sada zumunta Bello Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello, ya fitar da wani bidiyo a shafinsa na X da ke bayyana zargin gwamnatin ta Kano da bai’wa wani kamfani mai suna Novomed kwangilar sayen magunguna na naira miliyan 10 ga kananan hukumomin Jihar.

Bidiyon na Dan Bello da ya fitar ya zargi gwamnatin ta Kano da bai’wa ɗan uwan ga tsohon gwamnan Jihar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kwangilar siyan magungunan, inda kuma ya bayyana cewa a duk kowanne wata ƙananan hukumomin Jihar 44 na bayar da naira miliyan 10 ga kamfanin na Novomed mallakar Musa Garba Kwankwaso.

Bayan fitar da bidiyon na Dan Bello hakan ya haifar da cece-kuce da mayar da martani a shafukan sada zumunta tun bayan wallafa bidiyon.

To sai dai bayan wallafar bidiyon na Dan Bello gwamnan ya bai’wa shugaban Hukumar Korafe-Korafen Jama’a da Yaki da Rashawa ta Jihar, umarnin gaggauta gudanar da bincike akan zargi na Dan-Bello, tare kuma da bayar da rahoton sakamakon da aka samu akai domin daukar matakin da ya dace.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci Al’ummar jihar da su kwantar da hankulansu har zuwa lokacin da za a fitar da sakamakon binciken.

Leave a Reply

%d bloggers like this: