Jami’an sojin runduna ta daya a Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu ‘yan bindiga biyu a yankin unguwar Sarkin Musulmi da ke karamar a jihar Zamfara.

Mai magana da yawun rundunar Laftanar Sulaiman Omale ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi a garin Gusau babban birnin Jihar.
Jami’in ya ce jami’an sojin karkashin kwamadan runduna ta Daya ne su ka yi nasara akan ‘yan bindiga a wata musayar wuta da suka yi da su a karamar hukumar Kauran Namoda da ke Jihar a ranar 16 ga watannan na Augusta.

Kakakin ya kara da cewa jami’ansu sun kai daukin gaggawa bayan samun bayanan sirri kan ayyukan ‘yan ta’addan a cikin ƙaramar hukumar ta Kauran Namoda.

Kakakin ya ce bayan sojojin gurin sun yi musayar wuta da maharan, inda suka hallaka biyu daga cikinsu yayin da kuma sauran suka tsere dauke da raunuka a tare da su.
Inda kuma jami’an suka ƙwato babur guda ɗaya da suke amfani da shi wajen aikata ta’addanci.
Omale ya ce a halin yanzu jami’an rundunar hadin gwiwa ta sashe na 1 a yankin Arewa maso Yamma, ta Operation Hadarin daji na ci gaba da samun nasara a yaki da ta ke yi da ‘yan ta’adda a Jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma a Najeriya.
Sannan jami’an na ci gaba da gudanar da sitiri a yankin domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.