Shugabar ma’aikata a Najeriya Misi Didi Walson Jack ta ce babu wata kafa d za su ɗauki wani maaikaci da shi da ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa.

Misis Didi ta bayyana haka ne a Abuja yayin da ta ziyarci wajen rubuta jarrabawar ƙarin girma na ma’aikatan Najeriya a Abuja.
Misis Didi wadda sakataren dindindin a hukumar Mista Raymond Omachi ya wakilta.

Ta ce ya zama wajibi ma’aikatan gwamnati su samu ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa domin babu gurbin wani maaikaci da shi da ilimin.

A cewar shugabar, a halin yanzu gwamnatin tarayya ta mayar da hankali ne wajen ganin ta bi tsarin ma’aikata da ake yi a duniya.
Ma’aikata 12,444 ne su ka rubuta jarrabawar ƙarin girman a fadin Najeriya baƙi ɗaya.
Darakta a hukumar shirya jarrabawar shiga jami’a a Najeriya Jamb Funmilola B Usman wadda ta wakilci hukumar, ta ce ta gamsu da yadda aka shirya jarrabawar.