Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya miƙa saƙon taaziyya kan kisan gillar da ƴan bindiga su ka yi wa sarkin Gobir na jihar Sokoto.

Ƴan bindigan sun hallaka Alhaji Isa Bawa wanda hakimi ne na Gatawa a ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.


Tinubu ya yi alhinin mutuwarsa tare da nuna takicinsa.
Sannan ya ce za su tabbata an hukunta ƴan bindigan da su ka hallakashi.
Haka kuma ya mika taaziyyarsa ga masarautar Gobir da ma gwamnatin jihar
Shugaba Tinubu ya sake jaddada aniyarsa na tabbatar da tsaro a Najeriya tare da magance waɗanda su ka addabi kasar.
