Wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun yi garkuwa da dagacin Garu Kurama da ke ƙaramar hukumar Lere a jihar Kaduna.

 

An yi garkuwa da dagacin mai suna Yakubu Jadi da wasu mutane shida a ƙauyen Gurzan Kurama.

 

Daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su har da yar dagacin garin.

 

Kungiyar al’ummar kudancin Kaduna sun tabbatar da haka a wata sanarwa da su ka fitar mai dauke dasa hannun mai magana da yawunta

 

Su ka ce an yi garkuwa da dagacin ne tun a ranar Juma’a da ta gabata.

 

A cikin sanarwar, sun ce har zuwa yanzu yan bindigan ba su tuntubi kowa a kan yin garkuwa da dagacin da mutanensa ba.

 

A sakamakon haka su ka yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara kaimi wajen ganin an kubutar da su.

 

Jami’an yan sanda a Kaduna dai ba su tabbatar da lamarin ba zuwa yanzu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: